Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza, Haruna Kakangi da Mukhtar Adamu Bawa

time_stated_uk

  1. Ban-kwana

    Masu bibiyar mu a wannan shafi, a nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin da muke gabatar muku daga Najeriya da kuma sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, inda za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    Mukhtari Adamu Bawa ke cewa mu kwana lafiya

  2. Za mu bijire wa shirin ƙara kuɗin man fetur a Najeriya - 'Yan fafutuka

    oil pump

    Wata gamayyar ƙungiyoyin fararen hula ranar Juma'a ta ce za ta bijire wa shirin ƙara farashin man fetur da ake zargin ƙungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu ta Najeriya (IPMAN) na ƙoƙarin yi.

    Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ambato wata sanarwa da haɗin gwiwar, Dr Basil Musa da Mallam Haruna Maigida suka fitar na cewa za su bijirewa yunƙurin IPMAN, na ƙara farashin litar man fetur zuwa N700 ta hanyar rufe gidajen man IPMAN da ke faɗin Najeriya.

    Ƙungiyoyin dai sun haɗar da Oil and Gas Transparency and Advocacy Group da Civil Society Coalition for Economic Development (CED), da Centre for Citizens Rights da Centre for Good Governance Advocacy da kuma Action against Corruption in Nigeria, da sauransu.

    Sun dai zargi IPMAN da zama kishiyar gwamnati da ƙara tsanani a kan talakawan Najeriya, ta hanyar ƙarin farashin man fetur su kaɗai.

    Gamayyar ƙungiyoyin ya ce shirin ƙara farashin man abu ne da ba za a amince da shi ba, kuma sun yi kira ga gwamnatin tarayya ta dakatar da IPMAN daga abin da ta yi zargin cewa ci da gumin talakawan Najeriya ne.

    Sun kuma ce matakin wani zagon ƙasa ne ga tattalin arziƙin ƙasar don kuwa ya zo ne a daidai lokacin da 'yan Najeriya har yanzu ke ƙoƙarin farfaɗowa daga halin gigitar da suka shiga bayan ƙara farashin man fetur na ranar 29 ga watan Mayu.

    'Yan Najeriya da ma suna cikin mawuyacin hali in ji su, saboda ƙarin kuɗin man fetur na baya-bayan nan ba tare da ɓullo da matakan rage raɗaɗi ba.

    Sun dai lashi takobin gangamo wakilansu da sauran masu ruwa da tsaki a faɗin jihohin ƙasar 36 don gudanar da zanga-zanga, kuma a cewarsu zanga-zangar za ta mayar da hankali wajen garƙame gidajen mai a fadin Najeriya.

    A baya-bayan nan dai, wani jami'in IPMAN Bashir Ɗan Mallam ya shaida wa BBC cewa matakin nasu ya ta'allaƙa ne a kan farashin dalar Amurka, wanda idan ana samun dala cikin sauƙi farashin man fetur zai yi ƙasa, idan kuma dala ta yi wahala, ba shakka farashin mai zai tashi.

  3. Kotu ta ce mai zayyanar kwamfyuta ta yi daidai idan ta ƙi yi wa masu auren jinsi aiki

    Designer

    Kotun Ƙolin Amurka ta yanke hukuncin da ya bai wa wata mai zayyanar kwamfyuta (graphic design) gaskiya a shari'ar da aka shigar bayan ta ƙi buɗe wa wasu masu auren jinsi shafukan intanet.

    Lorie Smith, daga jihar Colorado, ta ce ba za ta iya yi wa masu auren jinsi aikin ba, saboda imaninta na addinin Kirista.

    Dokar jihar Colorado ta hana harkokin kasuwanci da ke hulɗa da jama'a su ƙi yin harka da wani ko wata, saboda zaɓinsu na neman jinsi.

    Sai dai Kotun Ƙolin Amurka a yanzu ta ce ba za a iya tursasa fasihai su zayyana saƙonnin da suka saɓa wa imanin addininsu ba.

    Muhimmin hukuncin na kotun ƙolin Amurka a ranar Juma'a ya yi wa 'yancin 'yan luwaɗi da maɗigo lam'a wajen neman a sayar musu da kaya, ko a yi musu wani aiki, ba tare da an nuna musu wariya a 'yancinsu na faɗar albarkacin baki ba.

    Duka alƙalan kotun shida masu ra'ayin gurguzu sun goyi bayan mai zayyanar kwamfyutar, yayin da sauran alƙalai uku masu ra'ayin kawo sauyi suka juya mata baya.

    Ra'ayi mafi rinjaye na kotun shi ne Shaɗarar Farko wato First Amendment, ta tsarin mulkin Amurka ta kare 'yancin fadar albarkacin baki, abin da ya hana jihar Colorado tilasta wa mai zayyanar ta wassafa saƙonnin da ba ta yarda da su ba.

  4. Ghana za ta shiga matsalar rashin lantarki tsawon mako ɗaya

    candle light
    Image caption: Kamfanonin 'yan kasuwa ne ke samar da kimanin 47% na wutar lantarkin da ake buƙata a Ghana

    Wasu 'yan ƙasar Ghana na iya aukawa cikin matsalar ƙarancin lantarki tsawon mako ɗaya, matuƙar cibiyar masu samar da lantarki mai zaman kanta ta cika alƙawari kan barazanar da ta yi.

    Za a fara ɗauke wutar lantarki ne daga ranar Asabar kuma lamarin zai iya kai wa tsawon kwana takwas a cewar Cibiyar Masu Samar da Lantarki masu Zaman Kansu ta Ghana (GCIPP), matuƙar gwamnatin ƙasar ta gaza biyan kuɗin da suke bi bashi har $1.9bn ya zuwa ranar Juma'ar nan.

    Ghana tana fama da matsalar tattalin arziƙi mafi muni a tsawon shekaru, don haka gwamnati ke fatan za ta rage kuɗaɗen ruwan da take biya a kan basuka.

    Kamfanoni masu zaman kansu ne ke samar da wutar lantarki kimanin kashi 47% a Ghana. Suna kuma samar da kashi 67% daga zafin iskar gari.

    Cibiyar GCIPP na neman gwamnati ta biya aƙalla kashi 30% na kuɗi $1.4bn da ake bin ta ya zuwa watan Maris, saboda yawan bashi ya kassara jarinsu da kuma ƙoƙarinsu na ci gaba da samar da lantarki.

    Masu samar da lantarkin tun da farko sun ƙi amincewa da wani ƙudurin gwamnati na jingine biyan bashin a wani ɓangare na matakan aiwatar da shirin ceton tattalin arziƙin Ghana na dala biliyan uku daga IMF.

  5. Farfesa Adamu Rasheed ya yi ban-kwana da hukumar kula da jami'o'i

    Prof Abubakar Rasheed

    Farfesa Abubakar Adamu Rasheed a hukumance ya miƙa aiki ga jami'i mafi girman muƙami a hukumar kula da jami'o'i ta Najeriya.

    Yayin wani taron miƙa al'amuran hukumar ga Mista Chris Maiyaƙi a Abuja ranar Juma'a, Farfesa Rasheed ya ce ya samu amincewar da ta wajaba daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kafin ya ajiye aiki ranar 30 ga watan Yunin, 2023.

    Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ambato shi yana cewa sabon babban sakataren riƙo ne zai ci gaba da gudanar da harkokin hukuma ya zuwa lokacin da shugaban ƙasa zai naɗa wani jami'i.

    ‘Saboda burin da nake da shi na shafe wasu shekaru a aji, na yanke shawarar rubuta wa shugaban ƙasa wasiƙa game da aniyata ta yin murabus ta hanyar ma'aikatar ilmi ta tarayya, shekara uku kafin ƙarewar wa'adina.

    ”Bayan amincewar ne, na rubuta takarda ga Shugaban Jami'ar Bayero Kano don ya ba ni dama na koma aji daga ranar Asabar 1 ga watan Yulin 2023.

  6. Kotun Amurka ta soke shirin yafewa ɗalibai bashin karatu

    US students

    Kotun Ƙolin Amurka ta soke ƙudurin Shugaba Joe Biden na yafe wa ɗaliban ƙasar bashin karatu na biliyoyin daloli da aka ba su.

    Hukuncin wanda ya samu rinjayen alƙalan kotun shida a kan uku da suka nuna amincewa ya rusa shirin gwamnati wanda za ta yafe wa duk ɗalibi kuɗi kimanin $10,000 - ga wasu ma har sama da $20,000.

    Kotun Ƙolin ta amince cewa shirin yana fama da rashin tabbas tun lokacin da wasu jihohi masu ra'ayin gurguzu suka shigar da ƙara, inda suka ƙalubalanci shugaban Amurka da cewa ya wuce ikon da doka ta ba shi.

    Hukuncin zai shafi bashin da Amurkawa fiye da miliyan 40 suka ci.

    Bayan sanar da hukuncin, kafofin labaran Amurka sun ba da rahoton cewa ana sa rai Shugaba Biden zai yi jawabi game da sabbin matakan kare masu cin bashi nan gaba a yau Juma'a.

    Jimillar bashin da gwamnatin tarayya ta bai wa ɗalibai ya ninka har fiye da sau uku a cikin shekara 15 da ta wuce, inda ya tashi daga kimanin dala biliyan 500 a 2007 zuwa dala tirliyan ɗaya da biliyan 600 a yau.

    Gwamnatin Joe Biden ta fuskanci ƙararraki daban-daban guda biyu, daya ta ƙunshi jihohi guda shida da jam'iyyar Rifablikan ke mulki - Nebraska da Missouri da Arkansas da Iowa da Kansas da kuma Karolina ta Kudu - sai kuma ɗayar wadda wasu ɗalibai guda biyu suka shigar.

    A duka shari'o'in biyu, masu ƙara sun ce ɓangaren zartarwa ba shi da ikon da zai yafe wa dumbin dalibai bashin karatu.

  7. 'Tsadar Aikin Hajji ta fi ƙarfin matashi ɗan Afirka iri na'

    A youth
    Image caption: Tashin farashin ibadar Hajji ta dusashe burin Ahmed Haji na ziyarar Ɗakin Allah a Makkah

    Matasa Musulmai a nahiyar Afirka sun ce tsadar kuɗin tafiya Aikin Hajji, na tauye musu damar zuwa ƙasa mai Tsarki don sauke farali.

    Hajji dai, ibada ce da Musulmai kan je ziyara biranen Makkah da Madina a Saudiyya aƙalla sau daya a rayuwarsu, idan sun samu dama.

    "Gaskiya raina yana ɓaci game da hakan. Ina kuma jin takaici a kan yadda mutane da yawa ba sa tattauna wannan batu na ƙarin tsadar kuɗin zuwa Hajji. Sai mu ga kamar Saudiyya da kamfanonin shirya tafiye-tafiye na cin ƙazamar riba daga wannan aikin ibada da muke son zuwa, kamar yadda addini ya shar'anta," a cewar wani ma'aikacin agaji ɗan shekara 24 a ƙasar Kenya.

    Ya ce ya yi ƙoƙarin tara kuɗi har sama da $3,000 kwatankwacin naira miliyan biyu bayan wani kamfanin shirya tafiya Aikin Hajji ya buƙaci ya tanadi hakan. Sai dai daga bisani, ga wani abu mai ban takaici da ruɗarwa, ba zato ba tsammani sai farashin ya ninka zuwa $6,000 kimanin naira miliyan huɗu.

    Aikin Hajjin bana a karon farko tun cikin shekarar 2019, ba a yi shi cikin matakan daƙile annobar korona ba, don haka adadin mutanen da suka halarci ibadar na da yawan ban mamaki, inda mutane sama da miliyan biyu daga ƙasa 160 suka gudanar.

    Sai dai tsadar kuɗin ibadar ta sanya burin Musulman duniya da yawa na zama tamkar mafarki.

    Wannan lamarin ya fi zama gaskiya musamman a Afirka, inda mizanin talauci ya zarce kashi 30%, abin da ya sa ta zama nahiyar da mafi yawan mutanenta ba sa samun damar zuwa Aikin Hajji a duniya.

  8. Shalkwatar tsaron Najeriya ta bai wa wasu manyan sojoji zuwa Litinin su yi ritaya

    s

    Shalkwatar tsaron Najeriya ta umarci manyan sojoji da suka haura kwas na 39 a makarantar horas da manyan sojoji da su ajiye aiki bisa raɗin kansu.

    Matakin na zuwa ne bayan da Bola Ahmed Tinubu ya naɗa sabbin hafsoshin tsaron ƙasar.

    Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwar mai ɗauke da sa hannun Manjo janar Y. Yahaya a madadin babban hafsan tsaron ƙasar.

    “An umarce ni na buƙaci duka manyan sojoji da ke sama da kwas na 39 na makarantar horas da manyan hafsoshin sojin ƙasar, su gaggauta miƙa takardun ajiye aiki bisa raɗin kai'', in ji sanarwar.

    “Haka kuma ana buƙatar waɗanda umarnin ya shafa su mika takardun nasu ga shalkwatocin tsaron da suke aiki zuwa ranar Litinin 3 ga watan Yulin 2023''.

    Bisa ga al'adar aikin soji, manyan jami'ai ba za su karɓi umarni daga sojojin da suka girma a aiki ba.

    Dan haka naɗin sabbin manyan hafsoshin tsaron da shugaban ƙasar ya yi, zai tilasta wa manyan sojoji kusan 100 ajiye aikinsu.

    Waɗanda suka haɗar da Janar-janar, da masu muƙamin Burgediya janar da masu muƙamin Air Vice Marshal da muƙamin Admirals a rundunonin sojin ruwa da na sama.

    Shi dai sabon babban hafsan tsaron ƙasar Manjo Janar Christopher Musa ɗan kwas na 38 ne na makarantar horar da manyan hafsoshin tsaro, yayin da sauran manyan hafsoshin sojin ƙasa na sama da na ruwa su kuma 'yan kwas na 39 ne.

  9. Yariman Saudiyya ya gana da manyan jami'an ƙasashen duniya da suka je aikin Hajji

    d

    Yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya Muhammad Bin Salman ya jagoranci taro da manyan jami'an gwamnatocin ƙasashen duniya da ke halatar aikin hajji.

    Taron - wanda Sarki Salman ke gudanarwa shekara-shekara - na samun halartar manyan jami'an gwamnatocin ƙasashen duniya da hukumomin gwamnati, da shugabannin hukumomin alhazai.

    Jaridar Saudi Gazzet ta ruwaito cewa ganawar wadda a ka yi a fadar Sarkin da ke birnin Makka, ta samu halartar sarkin Malaysia Al-Sultan Abdullah Ri’ayatuddin Al-Mustafa Billah Shah, da shugaban ƙasar senegal Macky Sall, da shugaban Pakistan Arif Alvi, da shugaban Bangladesh Mohammed Shahabuddin,da mataimakin shugaban ƙasar Maldives Faisal Naseem, da Firaministan Masar Dr. Mustafa Madbouly.

    e

    Sauran manyan shugabannin da suka halarci taron su ne Firaministan Lebanon Najib Mikati, da na Somalia Hamza Abdi Barre, da na Nijar Ouhoumoudou Mahamadou, da na Palestine Mohammad Ibrahim Shtayyeh, da shugabannin majalisun dokokin ƙasashen musumi da dama.

    A yayin da yake jawabi, Yariman na Saudiyya ya ce ''A kodayaushe masarautar Saudiyya na ƙoƙarin hidimta wa masallatai biyu masu alfarma, kuma a kodayaushe a shirye masarautar take wajen gudanar da wannan aiki''.

    Daga karshe Yariman ya taya mahajjatan bana murnar kammala aikin hajjinsu na bana, tare da fatan komawa ƙasashensu cikin kwanciyar hankali.

  10. MDD ta buƙaci Birtaniya ta jingine batun kai masu neman mafaka Rwanda

    Hukumar Kare Hakƙin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga gwamnatin Birtaniya ta sake tunani kan shirinta na kai masu neman mafaka zuwa ƙasar Rwanda.

    Kiran na zuwa ne bayan da kotun ɗaukaka kara da ke birnin Landan ta ce matakin haramtacce ne.

    Babban kwamishinan hukumar Volker Türk ya ce shirin na Birtaniya ya haifar da damuwa kan dokokin kare 'yancin bil adama da na 'yan gudun hijira.

    Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi maraba da hukucin kotun, tana mai cewa Birtaniya ta sake duba wasu hanyoyin, ciki har da haɗa hannu da ƙasashen Turai.

    Gwamnatin Birtaniya na shirin ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Kolin kasar, tana mai cewa tana da damar hana 'yan ci rani shiga ƙasar ta hanyar amfani da ƙananan jirage.

  11. Tsaron Najeriya ba abu ne mai sauƙi ba – Irabor

    dc

    Tsohon babban hafsan tsaron Najeriya Janar Lucky Irabor mai ritaya, ya ce samar da tsaro ga babbar ƙasa irin Najeriya ba abu ne mai sauki ba, amma kuma ya ce abu ne da za a iya cimmawa.

    Janar Irabor ya bayyana haka ne cikin wani jawabi da ya gabatar ranar Juma'a, a wajen taron karramawar barin aiki da aka shirya masa a barikin soji na Mogadishu Cantonment da Abuja babban birnin ƙasar.

    Ya ce akwai jan aiki mai yawa a gaban sojojin ƙasar na bai wa ƙasar tsaron da take buƙata.

    Ya kuma bayyana gamsuwarsa kan gudunmowar da ya bayar a aikin sojin ƙasar, yana mai cewa zai bar rundunar sojin ƙasar fiye da yadda ya same ta.

    Tsohon babban hafsan tsaron ya kuma yi kira ga 'yan ƙasar su guji aikata abubuwan da ka iya zubar wa rundunar sojin ƙasar kima.

    Yana mai cewa rundunar a shirye take domin kawo haɗin kai da zaman lafiya da kare rayukan 'yan ƙasar.

    Ya kuma yi fatan sabon babban hafsan tsaron zai ɗora a kan ciyar da rundunar sojin kasar gaba.

    A shekarar 2021 ne tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya naɗa Irabor a matsayin babban hafsan tsaron ƙasar wanda ya maye gurbin Abayomi Olonisakin.

  12. Dangote ya tallafa wa 'yan Najeriya da suka koma daga Sudan

    d

    Gidauniyar Aliko Dangote ta bayar da tallafi ga wasu 'yan Najeriya da yaƙin Sudan ya tilasta musu komawa ƙasar.

    Mutane 125 da suka koma Najeriya ranar Asabar da ta gabata suka haɗar da gajiyayyu, kowannensu ya samu tallafin naira 100,000 da wasu kayyakin ihsani a cikin jaka, daga gidauniyar ta Dangote.

    A cikin watan Mayu fiye da mutum 2,278 suka samu tallafin 100,000 kowannensu da abubuwan ihsani domin samun saukin haɗuwa da iyalansu, bayan dawo da su ƙasar daga Sudan.

    Daga cikin mutanen da aka kwaso cikin makon da ya gabata har da wasu tsofaffi biyu da suka yi shirin zuwa Umara a mota, hanya ta bi da su ta birnin Khartoum, suka kuma faɗa tarkon yaƙin da ake gwambazawa a birnin, lamarin da ya sa suka rasa duka guzurinsu.

    Wani dattijo mai suna Muhammad Saidu Ahmed ya ce ''Na dawo daga Sudan ba tare da ko sisi ba, amma yanzu na samu 100,000''.

    d

    Ita ma wata dattijuwa ta bayyana yadda ta rasa ɗanta sakamakon tashin bam a birnin Khartoum.

    Matar mai shekara 80 ta ce 'yan uwanta da dama sun tsere sakamakon hare-haren boma-bomai ba kaƙƙautawa a birnin Khartoum.

    s
  13. Ambaliyar ruwa ta kashe mutum bakwai a Afirka ta Kudu

    s

    Aƙalla mutum bakwai ne suka mutu, yayin da ake tsammanin adadin ka iya ƙaruwa, bayan da wata ambaliya ruwa ta afka wa lardin Kwazulu-Natal a Afirka ta Kudu.

    Ambaliyar ta yi ɓarna mai yawa a yankuna da dama a kudu maso gabashin lardin, bayan mamakon ruwan sama haɗe da iska mai ƙarfi da tsawa suka afka wa lardin a farkon mako.

    A birnin Durban an ceto gawarwakin wasu mata biyu ciki har da mai shekara 20 da wata ƙaramar yarinya.

    Akalla gidaje 70 ne suka rushe, yayin da fiye da mutum 150 suka rasa muhallansu, kamar yadda hukumomin lardin suka bayyana.

    Hukumar kiyaye aukuwar bakla'o'i ta ƙasar na ci gaba da auna irin ɓarnar da ambaliyar ta yi.

  14. Burkina Faso ta dakatar da gidan Talbijin na Faransa a ƙasar

    a

    Hukumar kula da kafafen yaɗa labarai ta Burkina Faso ta dakatar da gidan talbijin na French TV News daga aiki na tsawon wata uku, bisa zargin yaɗa labaran ƙarya kan rikicin masu ikirarin jihadi.

    Hukumar ta zargi gidan talbijin ɗin da yaɗa labaran da ke cewa masu ikirarin jihadin na samun ƙarfi a ƙasar, yayin da ya ce sojojin gwamnati na amfani da makaman da aka ƙera a cikin gida domin kare kansu daga hare-haren masu iƙirarin jihadin ke kai musu.

    A watan Afrilu gwamnatin kasar ta kori 'yan jaridar da ke aiki da kafofin yaɗa labarai na Le Monde da Liberation.

    Haka kuma ƙasar ta sanar da rufe gidajen radiyo na France 24 da RFI.

  15. Ana zargin gwamnatin Sokoto da cin zarafin jami'an tsohuwar gwamnatin jihar

    Ahmad Aliyu

    Jami’an tsohuwar Gwamnatin jihar Sokoto ta Aminu Waziri Tambuwal sun zargi gwamnati mai ci da fakewa da batun bincike wajen cin zarafi da yi musu bita-da-ƙullin siyasa.

    Hakan dai ya biyo bayan kamen da suka ce jami’an tsaron sun yi wa wasu tsoffin kwamishinoni ana tsaka da bukukuwan Sallah da sunan za a bincike su.

    Sabuwar gwamnatin Sokoton dai ta kafa kwamitoci daban-daban domin binciken gwamnatin da ta gada ciki har da wanda zai binciki yadda tsohuwar gwamnatin ta Aminu Waziri Tambuwal ta yi gwanjon wasu daga cikin kadarorin gwamnati a jihar.

    Sai dai bayan da kwamitin mai mutum 19, ya soma aikinsa na bincikar yadda tsohuwar gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal ta yi gwanjon kadarorin da suka haɗa da manyan motocin alfarma da sauran su, ake ta samun korafe-korafe daga ɓangaren tsohuwar gwamnatin.

    Alhaji Isa Bajini Galadanci, kwamishinan muhalli ne a lokacin tsohuwar gwamnatin ya shaida wa BBC cewa ba maganar ƙwace motoci ne ke damunsu ba, yadda ake wulaƙanta su da cin zarafinsu shi ne abin da ke ci musu tuwo a ƙwarya.

    Ya ce ''a yanzu alal misali sun kama mu mu uku, da ni da tsohon shugaban ma'aikata da tsohon kwamishin tsaron cikin gida, ba tare da gayyatarmu ba''.

    ''Kamar ni, na gama yankan ragunana (Layya) kenan, sai ga motoci kusan biyar da 'yan sanda da bindigogi suna harɓin iska, yadda ka san mutum ya kashe shugaban ƙasa.Kana tare da mutane cikin mutuncinka a zo a yi maka wannan'', in ji tsohon kwamishinan.

    Ya yi zargin cewa ɓata suna ne da cin zarafi da kuma wulaƙanci gwamnatin jihar ta yi musu, yana mai cewa gwanjon motocin aka yi musu suka saya, kuma suna da takardun shaida da ke nuna cewa sayen motocin suka yi.

    To amma gwamnatin jihar Sokoton, ta bayyana cewa babu wani abu da suka yi da ya saɓa wa doka, kamar yadda Malam Abubakar Bawa mai bai wa gwamnan jihar shawara kan kafafen yaɗa labarai ya shaida wa BBC.

    ''Maganar cewa an yi musu gwanjon motocin bisa ƙa'ida ba haka take ba, ba muna cewa ba a yin gwanjo ba ne, amma akwai matakai da ya kamata a bi wajen yin gwanjon kayan gwamnati'', in ji Mallam Bawa.

    Ya kuma musanta batun cewa sun tura jami'an tsaro domin cin zarafin jami'an tsohuwar gwamnatin.

    Jim kadan bayan hawansa kan kujerar gwamnan jihar a ƙarshen watan Mayu, Gwamnan Ahmad Aliyu na jihar ta Sokoto ya sanar da rusa duk wasu naɗe-naɗen mukamai da wanda ya gada Aminu Waziri Tambuwal ya yi ciki har da na sarautun gargajiya.

    Sannan kuma ya kakkafa kwamitoci daban-daban da za su binciki tsohuwar gwamnatin ta fuskoki daban-daban.

  16. MDD ta buƙaci ƙasashen duniya su gaggauta tallafa wa Haiti

    Shugabar hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ta bukaci ta kula da da mutanen Haiti, tana mai cewa ƙasar na cikin wani mawuyacin hali na buƙatar jin kai da ba a taɓa ganin irinsa ba.

    Da take yi wa 'yan jarida bayani bayan ziyarar da ta kai can, Catherine Russell ta ce masu aikata laifuka na amfani da fyade ga kananan yara da mata a matsayin makami wajen tsoratarwa da lalata daukacin al'umma.

    Ta ce yanzu haka gungun ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai ne ke riƙe da kashi sittin cikin ɗari na babban birnin ƙasar, Port-au-Prince, da sauran yankuna da dama.

    Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a tura dakaru na ƙasa da ƙasa domin dawo da zaman lafiya a Haiti, sai dai akwai jan kafa daga masu bayar da agaji ciki har da Amurka da Kanada.

    Rikicin ya ɓarke ne a ƙasar tun bayan kisan gillar da aka yi wa Shugaba Jovenel Moise shekaru biyu da suka wuce.

  17. An kama masu zanga-zanga fiye da 600 a Faransa

    e

    An kama sama da masu zanga-zanga aƙalla 667 yayin rikicin da ya ɓarke, bayan kisan gillar da 'yan sanda suka yi wa wani matashi mai shekara 17 a Faransa.

    A garuruwa da dama da suka hada da tsakiyar birnin Paris, an kona motoci da gine-gine tare da wawashe shaguna.

    An samu tarzoma mafi muni ne a Nanterre - inda aka harbe Nahel, mai shekaru goma sha bakwai dan asalin kasar Aljeriya.

    Dan sandan da ya harbe matashin ya yi da na sani, tare da neman afuwa.

  18. Ƙungiyar EU za ta yi taro kan alaƙa da China

    f

    A yau ne shugabannin ƙasashen Turai za su yi wani muhimmin taro a Brussels, inda ake sa ran batun China na kan gaba cikin muhimman batutuwan da za su tattauna.

    Ana sa ran wasu ƙasashe mambobin ƙungiyar za su ga baiken wasu daga cikinsu da ke ci gaba da ɗasawa da Beijing ta fannin tattalin arziki musamman Faransa da Jamus, da suka bayyana aniyarsu ta ci gaba da ƙulla hulɗar kasuwanci mai karfi da Chinar.

    Wannan batu dama ya jima yana haifar da rarrabuwar kawuna tsakanin ƙasashen Turan, inda da yawansu ke nuna damuwa game da dangantakar kut da kut da ke tsakanin Beijing ɗin da Rasha.

    Wasu daga cikinsu kuwa na fargabar kada dogaron su ga Chinar ya haifar musu da irin raɗadin da suka ji wajen raba gari da Rasha bayan ta ƙaddamar da mamaya a Ukraine

  19. Sallama

    Masu bin mu a wanna shafi barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a, da Hausawa ke yi wa laƙabi da Haji babbar rana.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a wannan safiya domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Kuna kuma iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.