Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nasidi Adamu Yahaya da Nabeela Mukhtar Uba

time_stated_uk

  1. Aisha Buhari 'na so a kawar da cututtuka masu yaduwa'

    Mai dakin shugaban Najeriya, Aisha Buhari, ta halarci wani taro kan tarin fuka da cututtuka masu yaduwa karkashin tawagar majalisar dinkin duniya.

    Tawagar na ziyara a Najeriya domin duba kokarin da ake wajen dakile cututtuka masu yaduwa da kuma tarin fika a Najeriya.

    Aisha Buhari ta wallafa jawabin a shafinta na Twitter ranar Laraba.

    Ta ce makasudin taron shi ne bayar da shawarwari kan yadda za a inganta hanyoyin hana bazuwar cututtukan da kuma rage masu dauke da tarin fuka.

    View more on twitter
  2. Bill Gates ya bayar da $10m don yaki da farin dango a Gabashin Afirka

    Gidauniyar Bill and Melinda Gates ta bayar da gudunmawar $10m domin taimaka wa wurin yaki da farin dango a yankin Gabashin Afirka.

    Za a mika kudin ne ga hukumar Abinci da Noma ta Majalisar Dinkin Duniya, wacce ta yi kira a bayar da agaji domin kawar da farin na dango wadanda suke barazanar haifar da matsalar yunwa.

    Shugaban hukumar QU Dongyu ya gode wa Gidauniyar bisa agajin da ta bayar sannna ya yi kira ga sauran attajirai su bayar da tasu gudunmawar domin kawar da farin dangon wadanda ke barazanar haifar da yunwa a yankunan da lamarin ya shafa.

    Mai kamfanin Microsoft., Bill Gates ne ya kafa Gidauniyar ta The Bill and Melinda Gates

    Za a bayar da kudin ne ga hukumar Abinci da Noma ta Majalisar Dinkin Duniya
    Image caption: Za a mika kudin ne ga hukumar Abinci da Noma ta Majalisar Dinkin Duniya
  3. Ana jana’izar marigayi Hosni Mubarak

    Ranar Laraba ake gudanar da jana’izar soji ga tsohon shugaban Masar, Hosni Mubarak, wanda ya mutu ranar Talata yana da shekara 91 a duniya.

    Za a binne gawar marigayin a makabartar da ake binne iyalinsa da ke gabashin birnin Alkahira bayan an yi jana’izarsa a masallacin Tantawy.

    Hukumomin kasar sun ayyana zaman makokin kwana uku kan mutuwar tsohon shugaban kasar.

    A shekarar 2011 aka hambarar da Mr Mubarak daga kan mulki lokacin wani bore.

    Marigayin ya shafe shekara 30 yana mulkin kasar bayan an hallaka marigayi tsohon shugaban kasar Anwar el- Sadat.

    Firai Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya yaba wa shirin Mr Mubarak na samar da zaman lafiya da tsaro

    Mubarak
    Image caption: Marigayi Mubarak ya shafe shekara 30 yana mulkin kasar
  4. Barkan mu da warhaka

    Da fatan kuna cikin koshin lafiya. Ku kasance tare da mu tsawon wannan rana ta Laraba, wadda Hausawa kan kira 'Tabawa ranar samu'. Za ku kawo muku labara da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da ma sassan duniya.

  5. Rufewa

    Duka-duka a nan muka kawo karshen labarai da rahotannin da muke wallafawa kai tsaye a wannan shafin.

    Idan Allah ya kai mu gobe, Laraba, za mu ci gaba da kawo muku wasu labarai da rahotannin.

    Za kuma ku iya duba kasa don karanta abubuwan da suka faru a Najeriya da sauran sassan duniya.

  6. Jam'iyya mai mulki a Malawi ta kulla kawance gabanin sabon zabe

    Daga Peter Jegwa Lilongwe, Malawi

    Jam'iyyar Democratic Progressive Party (DPP) mai mulki a Malawi ta kulla kawance da jam'iyyar United Democratic Front (UDF).

    Wannan na zuwa kasa da sa'oi 24 bayan da majalisar dokokin kasar ta zartar da wata doka, da ta sanya ranar 19 ga watan Mayu a matsayin ranar da za a gudanar da sabon zaben shugaban kasa, bayan da wata kotu ta soke nasarar Mista Peter Mutharika a zaben da aka yi a bara.

    Jam'iyyar UDF, wadda ta mulki Malawi tsakanin 1994 zuwa 2004, ita ce jam’iyya ta uku mafi girma, mai kujerun majalisar dokoki guda 10.

    DPP tana da kujera 61 sai babbar Jam’iyyar adawa a Malawi Congress Party mai kujeru 55.

    Atupele Muluzi, dan tsohon shugaban kasa Bakili Muluzi ne ke jagorantar UDF.

    Atupele Muluzi, ya yi aiki a gwamnatin Shugaba Mutharika kafin zaben da aka yi a Mayu wanda kotun tsarin mulki ta rushe a watan da ya gabata saboda matsalolin da aka fuskanta.

  7. 'Za a gina wa Yahudawa karin gidaje kafin zaben Isra'ila'

    Firai Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi alkawarin gina sabbin gidaje dubu uku da dari biyar ga Yahudawa 'yan kama wuri zauna a wani bangare mai matukar hadari da ke gabar yammacin Jordan.

    Ya ce tuni ya bada umarnin fitar da tsarin da ya kamata a yi amfani da shi wajen gina gidajen a wani wuri da ake kira E-1 da ke kusa da Jerusalam.

    A baya dai an yi ta nuna adawa da irin wannan shiri da Isra'ila ke aiwatarwa.

    Masu adawa da shirin na ganin cewa zai raba yankin na gabar yammacin Jordan zuwa gida biyu.

    Sai dai masharhanta na ganin matakin Mista Netanyahu wata dama ce da za ta kara masa farin jini a wajen jama'ar kasar yayin da ya ke tunkarar zabe a mako mai zuwa.

  8. An rufe makarantu a Masar saboda mamakon ruwan sama

    An rufe makarantu da jami'oi a sassan Masar saboda mamakon ruwan sama.

    An dauki matakin domin taimaka wa mutane, a cewar Firai Ministan kasar Mostafa Madbouly.

    Mamakon ruwan saman da aka fara ranar Litinin da safe ya haifar da ambaliyar ruwa a muhimman tituna tare da janyo cunkoson ababen hawa.

    Hukumar kula da yanayi ta kasar ta ce za a ci gaba da fuskantar ruwan sama mai karfi a sassan kasar.

    Masu amfani da kafafen sada zumunta sun wallafa hotuna da bidiyo kan ta'adin da ruwan saman ya yi.

    View more on twitter

    Wasu kuma sun caccaki gwamnati saboda rashin yin tanadi yayin da ambaliyar ruwa kusan kowace shekara take durkusar da harkoki a babban birnin kasar da wasu muhimman birane.

    A watan Oktoba, mutum takwas har da yra hudu sun mutu saboda ruwan sama mai karfi.

  9. Shugaba Buhari ya je jihar Ondo

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Ondo domin kaddamar da wata cibiyar masana'antar Linyl da kuma gadar sama ta Ore.

    Mataimaki ga shugaba Buhari kan yada labarai, Buhari Sallau ne ya wallafa a shafinsa na Twitter.

    View more on twitter
  10. Shugaban majalisar dokokin Kaduna ya yi murabus

    Shugaban majalisar dokokin jihar Kaduna da ke Najeriya, Aminu Shagali, ya yi murabus daga kan kujerarsa.

    Ba a bayyana dalilin saukarsa daga kan kujerarsa ba, amma wani bayani da gwamnan jihar Nasiru El-Rufai ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya taya murna ga Yusuf Zailani, wanda ya ziyarce shi bayan an zabe shi a matsayin sabon shugaban majalisar dokokin.

    Bayanai sun nuna cewa Zailani na hannun damar Gwamna El-Rufai ne.

    View more on twitter
  11. An kama Sanata a Kenya kan kalaman kiyayya

    Daga Ferdinand Omondi BBC News, Nairobi

    An kama wani dan majalisar dattawa a Kenya bayan an zarge shi da furta kalaman kiyayya a wata hira ta talbijin.

    Masu bincike sun jagoranci Ledama Olekina, sanatan yankin Narok zuwa ofishin hukumar hadin kan kasa domin yi masa tambayoyi.

    Hukumar tana da ikon gurfanar da duk wanda ake zargi da nuna wariya ko tayar da rikici a kan wata kabila ko mabiya wani addini.

    Masu suka sun ce hukumar ba ta da wani karfi kuma har yanzu ta kasa hana 'yan siyasa furta kalamai masu cike da takaddama.

    A hirar ta talbijin, Mr Olekina ya soki wasu al'umomi da ke neman shugabanci a yankin da kabilar Maasai suka fi yawa.

    Mr Olekina ya kare kalaman nasa inda ya ce yana magana ne a madadin jama'arsa wadanda tsawon shekaru ake take su sannan 'yan siyasa suke kwace musu filaye.

    Amma masu caccakarsa sun ba da misali da kundin tsarin mulkin Kenya wanda ya bai wa 'yan kasar damar zama da aiki da kuma mallakar dukiya a kowane bangare na kasar.

    Wasu kuma sun ce kalaman nasa na iya haifar da rikicin kabilanci.

  12. Labarai da dumi-dumiOlisa Metuh zai sha daurin shekara bakwai a gidan yari

    Wata babbar kotu da ke Abuja, babban birnin Najeriya ta yanke hukuncin daurin shekara bakwai kan tsohon kakakin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Olisa Metuh.

    Kotun ta yanke masa hukuncin ne bayan ta same shi da laifin almundahanar N400m.

    Da yake yanke hukunci a yau, alkalin kotun, Mai shari'a Okon Abang, ya ce ya samu tsohon jami'in na PDP ne da laifin halatta kudin haramun.

    Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa ce ta shigar da shi kara, inda ta zarge shi da karbar kudin daga hannun tsohon mai bai wa shugaban kasar shawara kan sha'anin tsawo, Kanar Sambo Dasuki.

  13. Coronavirus ta kama ministan lafiya

    Karamin ministan lafiya a Iran ya kamu da cutar Coronavirus yayin da cutar ke ci gaba da bazuwa a kasar.

    Adadin wadanda suka mutu bayan kamuwa da cutar ya kai mutum 15.

    Akwai rahotannin da ke cewa adadin wadanda suka mutun ya zarta haka.

    A birnin Qom na Iran ne cutar ta fara bulla wanda kuma birni ne da mabiya mazhabar Shi’a a fadin duniya ke zuwa ziyara a-kai-a-kai.

    Haka ma an samu rahotannin bullar Cutar Covid-19 a kasashen Afghanistan da Iraqi da Bahrain.

    A yanzu ana fargabar bullar cutar a sauran kasashen da ke makwabtaka ganin yadda matafiya ke baluguro a yankin.

    Adadin wadanda suka mutu bayan kamuwa da cutar ya kai mutum 15.
    Image caption: Adadin wadanda suka mutu bayan kamuwa da cutar ya kai mutum 15
  14. 'Yan majalisar dattawan Najeriya na so a kafa sansanin soji a Garkida

    Majalisar dattawan Najeriya ta nemi rundunar sojin kasar ta kafa sansanin soji a yankin Garkida da ke jihar Adamawa.

    Mayakan da ake zargi na kungiyar Boko Haram ne sun sha kai hari a garin na Gakirdam inda ko a makon jiyar sai da suka fatakki mutane daga garin bayan sun kashe wasu daga cikinsu.

    Amma a zamanta na ranar Talata, majalisar dattawan ta ce kafa sansanin soji a yankin zai kawo karshen yawan hare-haren da ake kai wa a garin.

    View more on twitter
  15. Ministocin EU sun amince da tsarin Birtaniya na tattaunawar kasuwanci

    Ministocin Tarayyar Turai sun nuna yardarsu kan tattaunawa da Birtaniya bayan da kasar ta fice daga EU.

    Daftarin - wanda majalisar kula da harkokin Tarayyar Turai ta amince da shi ranar Talata - zai zama tushen tattaunawar da Michel Barnier zai jagoranta.

    Ya ce ya kamata ka'idojin EU su zama abin dubawa kan duk wata yarjejeniyar kasuwanci a nan gaba.

    A hannu guda kuma, ministocin Burtaniya sun amince da matakin da gwamnati ta dauka na tattaunawar, wadda aka fara a ranar Litinin.

    Za kuma a wallafa yarjejeniyar a intanet sannan a gabatar da ita gaban majalisa ranar Alhamis.

    Tarayyar Turai
    Image caption: Micheal Barnier zai jagoranci tattaunawa da Birtaniya kan alakar kasuwanci a nan gaba
  16. 'Za a shawo kan Coronavirus a Iran'

    Shugaban Iran ya bukaci 'yan kasar su kwantar da hankalinsu yayin da ake kokarin dakile bazuwar sabuwar cutar numfashi ta Coronavirus.

    Hassan Rouhani ya bayyana cewa kasar za ta shawo kan cutar wadda ta kashe akalla mutum 16.

    Iran ta ruwaito mutum 95 da suka kamu da cutar ta Covid-19 tun makon jiya amma ana tunanin adadin ya zarce haka.

    Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce abin damuwa ne yadda ake samun karuwar cutar.

    WHO ta ce za ta aike magunguna da sauran kayan gwajin cutar ga Iran waadanda ake sa ran isarsu kasar nan da kwana daya ko biyu.

    Shugaba Rouhani ya yi kira ga mutane da su kiyaye shawarwarin da ma'aikatar lafiya ta ba da.

    Rouhani
  17. An kashe 'yan sanda sanadiyyar harin kwanton bauna a Burkina Faso

    'Yan sanda a Burkina Faso sun ce mutum hudu sun mutu sakamakon harin kwantan bauna da aka kai arewacin kasar.

    Mutum uku daga cikin wadanda suka mutu 'yan sanda ne. Sauran biyar din kuma sun jikkata.

    An kai harin a yankin Pissila zuwa Gibga da ke Lardin Sanmatenga a yankin Centre-Nord a arewa maso gabashin kasar.

    Ko a ranar Talatar da ta gabata ma, sojoji uku sun mutu a yankin kusa da kan iyaka da Mali.

    Burkina Faso dai na fama da rikicin masu da'awar kishin addinin Islama inda sama da mutum dubu hudu suka mutu a shekarar da ta gabata.

  18. An samu barkewar amai da gudawa a Mozambique

    Daga Jose Tembe BBC News, Maputo

    An tabbatar da mutuwar mutum 20 sakamakon barkewar amai da gudawa a arewacin Lardin Cabo Delgado mai arzikin iskar gas da ke Mozambique, a cewar jaridar Noticias.

    Hukumomin lafiya sun sanar da barkewar cutar a guduma uku na Cabo Delgado - Macomia da Mocimboa da Praai da kuma Ibo.

    Daraktar lafiya a Lardin, Anastacia Lidimba, ta ce barkewar ta faro ne daga wani tsibiri inda mutane suke samun mafaka a waje mara tsafta sakamakon tserewa hare-haren masu da'awar kishin Islama.

    Ta ce lamarin ya kazanta a tsibiran Matemo da Congo.

    Dr Lidimba ta ce kawo yanzu an gano mutum 273 da suka kamu da cutar.

    Tuni aka tura tawagar likitoci da ma'aikatan lafiya zuwa yankunan da cutar ta barke.

    Mozambique
  19. Kenya ta haramta yanka jakuna

    Daga Peter Mwangangi BBC News, Nairobi

    Ministan aikin gona a Kenya ya haramta yanka jakuna tare da ba da umarnin rufe duk wata mayankar jakuna da ke kasar.

    Peter Munya ya bai wa mamallaka mayankar jakuna hudu da ke kasar wa'adin wata daya su koma yanka sauran dabbobi irin su shanu da akuyoyi.

    Ministan ya ce za a rufe kasuwancin mutanen da suka ki bin umarnin.

    Sanarwar Mr Munya ta zo ne ranar Litinin bayan ya yi magana da tawagar manoman da suka yi zanga-zanga a wajen harabar ofishin ma'aikatar.

    Jakuna
  20. Labarai da dumi-dumiKotu ta samu tsohon kakakin PDP Oliseh Metuh da laifin sace N400m

    Wata babbar kotu da ke Abuja, babban birnin Najeriya, ta samu tsohon kakakin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Olisa Metuh, da laifin almundahanar N400m.

    Da yake yanke hukunci ranar Talata, alkalin kotun, Mai shari'a Okon Abang, ya ce ya kama tsohon jami'in na PDP ne da laifi guda daya - na halatta kudin haramun.

    Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa ce ta shigar da shi kara, inda ta zarge shi da karbar kudin daga hannun tsohon mai bai wa shugaban kasar shawara kan sha'anin tsaro, Kanar Sambo Dasuki.

    Gidan talbijin na Channels TV ya ambato Mai shari'a Abang yana cewa “Ra'ayina shi ne Metuh ya karbi N400m daga ofishin mai bai wa shugaban kasar shawara kan sha'anin tsaro ba tare da wata hujja ta kwangila ba; don haka an same shi da laifi daya na halatta kudin haramun.”