Isa ga babban shafi

Sojin Mali 3 da 'yan ta'adda 7 sun mutu a wani fada tsakanin bangarorin biyu

Akalla Sojin Mali 3 suka mutu yayinda wasu 5 suka jikkata yayin wata arangama tsakaninsu da ‘yan ta’addan da ke ikirarin jihari a tsakiyar kasar.

'Yan ta'adda na ci gaba da cin karensu ba babbaka a yankin saharar Afrika.
'Yan ta'adda na ci gaba da cin karensu ba babbaka a yankin saharar Afrika. AFP - SIA KAMBOU
Talla

Sanarwar da Rundunar Sojin Mali ta fitar cikin dare ta bayyana cewa an gwabza fada tsakanin dakarun Sojin da ‘yan ta’addan ne jiya talata a garuruwan Mopti da Segou wanda ya kai ga nasarar kisan batagarin 7.

Gwabzawar ta gaba da gaba a jiya na zuwa ne bayan mabanbantan hare-haren sari ka noke da ‘yan ta’addan ke ci gaba da kaiwa dakarun Sojin ta hanyar dasa musu nakiya a kan hanya lamarin da ke haddasa asarar rayuka tarin jami’an tsaron.

Kasar ta Mali na fama da rikicin kusan shekaru 11 ta yadda ‘yan ta’adda da ke ikirarin jihadi ke kwace iko da wasu yankuna tare da farmakar sassan kasar lamarin da ya haddasa asarar rayukan dubunnan mutane ciki har da tarin jami’an tsaro baya ga tilastawa wasu miliyoyi barin muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.